19 Yuni 2021 - 19:12
Iran : An Fara Kidayar Kuri'u Zaben Shugaban Kasa

A Iran, an rufe runfunan zaben shugaban kasa a cikin daren jiya bayan shafe sa’o’I 19 na kada kuri’a.

ABNA24 : An dai tsawaita kada kuri'ar don karbar masu jefa kuri'a dake cikin layin dake tafiya sannu a hankali, Sakamakon matakan da aka gindaya na kiyaye ka'idoji na kiwon lafiya dake nasaba da anobar cutar korona.

Tuni dai aka fara kirga kuri'u, Kuma ana sa ran ma’aikatar cikin gida ta kasar za ta fara bayyana sakamakon zaben sannu a hankali yayin da ake kidaya kuri’un.

Yan kasar kimanin miliyan 60 ne suka tantanci kada kuri’a a zaben wanda shi ne karo na 13 tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar.

‘Yan takara hudu ne ke fafatawa, domin maye gurbin shugaba Hassan Rohani, wanda ke kan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.

342/